Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaban Cocin Katolika na Duniya Fafaroma Benedict ya mutu
Tsohon shugaban Cocin Katolika na Duniya Fafaroma Benedict na 16 ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.
Kakakin fadar Vatican, Matteo Bruni ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN:2023: PDP za ta yi maganin Wike da wasu idan Ɗan takarar su ya bayyana – Tambuwal
Sanarwar ta ce, “Cikin bakin ciki na sanar da ku cewa Paparoma Emeritus, Benedict na 16, ya rasu yau da karfe 9:34 a gidan ibada na Mater Ecclesiae da ke fadar Vatican.”
Idan za’a tuna cewa Fafaroma Benedict a shekara ta 2013 ya zama Fafaroma na farko da ya yi murabus a matsayin shugaban Cocin Katolika na Duniya, tun tsakiyar zamanai da aka yi.
A wani labarin kuma: INEC Tace Har Yanzu Akwai Katin Zaɓe Sama Da Miliyan 1.7 Da Ba’a Karɓa Ba A Wata Jahar Kudu
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta ce katinan zabe na dindindin guda 1,693,963 da ba a karba ba a jihar Legas.
Sabuwar takarda daga ofishin hukumar da ke Legas da wakilinmu ya samu a ranar Asabar din da ta gabata ta kuma bayyana cewa, a ranar 29 ga watan Disamba, 2022, jimillar kayayyakin PVC da aka tattara sun kai 5, 816,528.