Ana sa ran za a gudanar da jarrabawar kammala manyan makarantun Sakandare da hukumar kala shirya jarabawar ta yammacin Afirka WAEC ke shirya wa a tsakanin ranar 8 ga Mayu zuwa 23 ga watan Yunin shekarar nan. Kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Shugaban Hukumar WAEC Mista Patrick Areghan ne ya bayyana haka a taron share fage na shirye-shirye kan jarrabawar da aka yi ranar Alhamis a Legas.
Akwai karin bayani…………
Areghan ya ce, Akalla mutane 1,621,853 ne suka yi rajista a makarantun gwamnati da masu zaman kansu 20,851.
A wani labarin kuma, Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane 131 Da Aka Sace, Da Karin ‘Yan Matan Chibok – DHQ
Shelikwatar tsaro ta ce dakarun Operation Hadin Kai, a cikin makonni biyun da suka gabata, sun ceto mutane 131 da aka sace, ciki har da wasu karin ‘yan matan makarantar sakandiren Chibok guda biyu a wani sumame da aka yi a yankin Arewa maso Gabas.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis din nan a Abuja a taron manema labarai na mako biyu kan ayyukan rundunar