Wani mai goyon bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ya fadi ya mutu a yayin babban taron jam’iyar Dake cigaba da gudana yanzu haka yau Asabar.
Magoya bayan ya nufi dandalin Eagle Square, wurin taron, idan ya fadi ya rasu.
Daya daga cikin wadanda ke kusa da shi ya ce marigayin ya fara korafin cewa yana ganin Jiri ne kafin daga bisani ya fadi.
Wakilin Jaridar Daily Trust a wurin ya shaida yadda da yawa daga cikin magoya bayan jam’iyyar sun Kai masa agajin gaggawa, don taimaka masa, amma hakarsu Bata cimma ruwa ba.
Daga baya wasu mutane karkashin jagorancin wasu jami’an tsaro suka tafi da marigayin.
Akwai Karin bayani…….