Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani dan majalisa mai suna Ishaya Bakano mai wakiltar karamar hukumar Song a jihar Adamawa.
Gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan dan majalisar da ke garinsu, Bannga, da sanyin safiyar Asabar, inda suka harbe dansa tare da lallasa shi kafin su kashe shi bayan ‘yan sa’o’i.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Sufetan ‘yan sandan jihar Adamawa Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, jami’an tsaro na yin duk mai yiwuwa don kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika, kuma ‘yan sanda na binciken kisan.
Bakano ya kasance har zuwa rasuwarsa mataimakin shugaban karamar hukumar Song. Ya wakilci Gudu Mboi Ward a Majalisar.
Ko da yake ana ci gaba da gudanar da bincike, akwai hasashen cewa an kashe shi.
Dan nasa da aka harba yana kan jinya a asibiti.
Adamawa dai ta sha fama da hare-hare da kashe-kashe a yan kwanakin nan.
Kisan Bakano dai shi ne na baya-bayan nan a irin wannan yanayi kuma yana faruwa ne ‘yan makonni bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe wani malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa a gidansa da ke karamar hukumar Girei ta jihar Adamawa.
A ranar 6 ga watan Yuli, wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan Reverend Daniel Umaru na Cocin The Brethren, Njairi a karamar hukumar Mubi, inda suka harbe limamin cocin, da kuma kashe ‘ya’yansa maza biyu, tare da sace ‘yarsa mai shekaru 13.
A wani labarin kuma na daban.
Wani likita mazaunin Landan, Obinna Obeta, an tsare shi bisa zargin hada baki da Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice domin saukaka tafiyar Ukpo Nwamini David zuwa Birtaniya domin cire masa koda.
Idan zaku iya tunawa tuna JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito a ranar 21 ga watan Yuni ne rundunar ‘yan sandan birnin London ta kama ma’auratan bisa zargin shirin cire kodar David don dasawa ‘yarsu Sonia da ke fama da ciwon koda.
David wanda a baya ya yi ikirarin cewa yana da shekaru 15 a duniya, a ranar 5 ga watan Mayu, 2022, ya gabatar da kansa a ofishin ‘yan sanda na Staines yana zargin Ekweremadu ya dauke shi zuwa Burtaniya ne don cire masa koda.
A daya bangaren kuma, Obeta ana zarginsa da hada baki da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa domin shirya ko saukaka tafiyar David zuwa Birtaniya da nufin yin amfani da shi ta hanyar cire wani bangare na sassan jikin sa.
Likitan mai shekaru 50 na Hillbeck Close, Southwark, kudu maso gabashin London ya bayyana a kotun Majistare ta Bexley a ranar 13 ga watan Yuli.
David wanda a baya ya yi ikirarin cewa shi karami ne, ya kuma shaida wa kotun Burtaniya cewa shi dan shekara 21 ne. Har yanzu Ekweremadu da matarsa suna tsare.