Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sako hakimin kauyen Zira da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi, Yahya Abubakar da dansa Habibu daga hannunsu.
A safiyar Talata aka sake su kuma an sake hada su da danginsu.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai farmaki garin Zira da misalin karfe 2 na safiyar ranar Asabar inda suka yi awon gaba da hakimin kauyen da dansa.
Ba a dai tabbatar ko an biya kudin fansa daga iyalan shugaban kauyen kafin a sake su ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya tabbatar da sakin mutanen ga manema labarai a Bauchi a ranar Talata.
Ya ce, “A yau, sarkin kauyen Zira da dansa sun sami ‘yanci. Dukkansu biyun suna cikin koshin lafiya.”
Wakil bai yi karin bayani kan sakin nasu ba.
Wakilin majiyar jaridar Dimokuradiyya ya ruwaito cewa, sakin nasu na zuwa ne sa’o’i kadan bayan an kubutar da tsohon babban sakataren hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Alhaji Sani Toro, tsohon mataimakin kociyan Super Eagles, Garba Yila, da kuma wani mutum guda bayan an yi garkuwa da su.