Abin da ya rage, kwana biyu a gudanar da zaben majalisar dokokin jihar Edo, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar, Jarret Tenebe, an kama shi bisa umarnin mataimakin gwamnan jihar, Hon. Philip Shaibu kamar yadda Leadership ta rawaito.
An ce an kama shi ne a garin Ikabigbo da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar, saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hauhawar Farashin Abinci Ya Haifar Da Rashin Tsaro, Sauyin Yanayi – FG
Tenebe shahararren mai fafutukar kawo wa jam’iyyar APC ƙuri’u ne, kuma babban mai biyayya ga Kwamared Adams Oshiomhole. Kwanakin baya ya zargi mataimakin gwamnan kan batutuwa daban-daban a wani faifan bidiyo.
Ita ma jam’iyyar adawa ta APC a wani taron manema labarai a birnin Benin a ranar Talatar da ta gabata, ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta shirya yin magudi a zaben majalisar dokokin jihar da za a yi ranar Asabar ta hanyar amfani da ‘yan daba.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Kanal David Imuse (rtd) da mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Ofure Osehobo, duk sun tabbatar da kama Tenebe amma har yanzu ‘yan sanda ba su amsa tambayoyi ba, musamman yadda jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Chidi. Nwabuzor, yaƙi daukar kira har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
A wani labarin kuma, Abin Da Zan Yi Idan Tinubu Ya Gayyace Ni Cikin Gwamnatinsa – Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce ba zai amince da duk wani tayin zama a cikin gwamnatin Bola Tinubu ta hadin kan kasa ba.
Obi ya maka Tinubu, zababben shugaban kasa da jam’iyyarsa ta APC a gaban kotu kan sakamakon zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.