Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama wani sansanin otal da ake amfani da ‘yan mata matasa a matsayin bayi.
Kimanin ‘yan mata 35 da aka yi amfani da su wajen tilastamusu yin jima’i na domin samun kudi, inda aka kubutar da su yayin da biyar daga cikinsu aka tabbatar suna dauke da juna biyu.
An ajiye ‘yan matan ne a otal din da aka yi amfani da su wajen yin lalata da su kuma an biya kudin dayakamata abiyasu da ake kira kudin “Madam”,.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma kama wasu mutane uku da suka hada da mataimakin manajan otal din, tare da kwato bindigogi guda uku da harsashi guda bakwai.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Tochukwu Ikenga, yayin da yake gabatar da ‘yan matan da wadanda ake zargin a ofishin ‘yan sandan yankin, Onitsha, a ranar Laraba, ya bayyana sunan otal din da Gally Gally Hotel, da ke Nkpor, kusa da Onitsha a, jihar Anambra.
“Wadanda aka kama da ‘yan matan da aka ceto a halin yanzu suna ofishin ‘yan sanda da ke Onitsha, inda ake yi musu tambayoyi” inji shi.