Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sauke dukkan kwamishinoninsa daga muƙaman su.
Wannan lamarin ya auku ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2022, inda ya sanar da hakan a wata takarda da gwamnan ya fitar a shafinsa na Facebook da Twitter.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ku Kammala Zaben Fidda Gwani Nan Da Wata Daya Ko Kuma Kuna Cikin Hatsarin Rashin Cancanta – INEC Ga Jam’iyyu
Takardar wadda Babban Sakataren Harkokin Mulki da Ayyuka na musamman Danjuma Ali ya sanyawa hannu a madadin Sakataren Gwamnatin Jahar, an fitar da ita ga Manema labaru.
A cewar gwamnan, ya yi hakan ne domin bai wa duk masu burin tsayawa takarar wata kujerar siyasa fitowa su tsaya ba tare da sun karya doka ba.
Sanarwar ta buƙaci dukkanin Kwamishinonin dasu miƙa harkokin Mulkin su ga Manyan Sakatarori a Ma’aikatun su.
A takardar, Gwamna Zulum ya godema su akan irin namijin ƙoƙarin da suka yi wajen cigaban Jahar.