By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya amince da raba kayan bikin Kirsimeti ga ma’aikata da daliban manyan makarantu afadin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Kenneth Ugbala ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya rabawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya ranar Alhamis a Abakaliki.
Ugbala, a cikin sanarwar, yace amincewar raba kayan ta yi daidai da ‘girmama Gwamna’ a matsayinsa na uban jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Duk ma’aikatan gwamnati da ’yan fansho a Ebonyi zasu karbi buhunan shinkafa mai nauyin 5kg guda biyu da kuma kudi Naira 10,000 da za a biya su ta asusun biyan albashin su.
“Duk ma’aikatan karamar hukumar suma zasu karbi buhunan shinkafa 5kg guda biyu, da tumatir din kayan hadi da kudi naira 5,000 da za a biya su suma ta asusun albashin su.
“Duk ma’aikatu da hukumomin mallakar gwamnatin tarayya an ba su tallafin Kirsimeti ta hannun shugabanninsu.
“An kuma baiwa ma’aikata da daliban manyan makarantun tarayya da na jihohi tallafin Kirsimeti suma ta hannun shugabanninsu.”
Sakataren gwamnati jihar ya godewa gwamnan bisa karamcin da ya yiwa jama’ar jihar.