Kasar Birtaniya ta sabunta sanarwar tsaro ga ‘yan kasarta dake zuane a Najeriya musamman a birnin tarayya Abuja. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Makwanni biyu da suka gabata Burtaniya ta sanar da cewa ‘yan ta’adda na iya kai hari a babban birnin tarayya Abuja nan ba da jimawa ba, inda ta shawarci ‘yan kasar da su guji tafiye-tafiye zuwa babban birnin Najeriya.
KARANTA WANNAN LAVARIN: Gwamna Bagudu Ya Amince Da Sakin Miliyan 60 Ga Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kebbi United FC
Sai dai kuma, a sabon sanarwar da ta yi a shafinta na yanar gizo a yammacin ranar Litinin, kasar ta ce: “Hukumar kula Harkokin Waje, Da Ofishin dake kula cigaban kasashen renon Ingila wato Commonwealth & Development Office (FCDO) a turance, ba ta ba da shawara kan iya shiga kowani yanki ba face zuwa Babban Birnin Tarayya. amam ta ce, haryanzu akwai hadarin kai hare haren yan ta’adda.
“Shawarar FCDO game da tafiya zuwa wasu yankuna na Najeriya na nan daram”
Ofishin na FCDO, a cikin wata sabon sanarwar da ta fitar, ta ba da shawarar hana duk wani tafiya zuwa jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Kaduna, Katsina, Zamfara, Delta, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross River.
Har ila yau FCDO ta ci gaba da ba da shawarar ta kan kauracewa duk wani balaguron balaguron tafiya zuwa jihohin Bauchi, Kano, Jigawa, Neja, Jihar Sakkwato, Jihar Kogi, mai nisan kilomita 20 daga kan iyakar Nijar da jihar Kebbi, jihar Abia, da yankunan da ba na kogin Delta ba. , Jihohin Bayelsa da Ribas, Jihar Filato da Jihar Taraba.
“Idan kanada wani shiro na tafiya zuwa wata kasa daga Birtaniya, Yakamata Ka jadawalin shawarar da muka fitar.” Inji sanarwar
A WANI LABARIN KUMA: Mambobin PDP 300 Sun Kara Mai Zuwa Jam’iyyar APC Mai Mulki
Wani tsohon jigo a jam’iyyar PDP a jihar Ondo, Gbenga Akinmoyo, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubarka, ba zai iya hada kan kasar nan ba idan aka zabe shi a 2023.
Akinmoyo, ya ce gazawar da ‘yan takarar shugaban kasa suka yi wajen hada kan jam’iyyar gabanin zabe alama ce ta mugun nufi.
Tsohon jigon jam’iyyar, wanda ya jagoranci mambobin jam’iyyar sama da 300 sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar, ya lura cewa dan takarar ba dan takara ba ne mai mai da hankali.