Zaɓen Kaduna: Ƴan takara hudu sun janye wa na APC
‘Yan takara hudu sun janye wa ɗan takarar (APC), Mista Jesse David Tanko, gabanin zaben fidda gwani na dan majalisar wakilai na mazabar Chikun na jihar Kaduna.
‘Yan takara hudu sun hada da Zipporah Samuel Bijeh na jam’iyyar Accord, David Sunday na Zenith Labour Party, Idris Inuwa na Social Democratic Party da David Ogah Batholomew na All Progressives Grand Alliance.
Idris Inuwa ya sanar da hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zaben Cike Gurbi: INEC ta fara rabon kayan zaɓe a Bauchi
Da yake jawabi a madadin ‘yan takarar hudu, ya bayyana cewa, “Duba da kyawawan halayen jagoranci da Gwamna Uba Sani ya nuna a jihar Kaduna, muna da tabbacin cewa a majalisar dokokin jihar APC muna da yakinin cewa za a gudanar da ayyuka da sauran su abubuwan da za su amfanar da jama’armu za su samu sauki, shi ya sa muka hadu mu marawa dan takarar jam’iyyar APC goyon baya a zaben da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.”
Ya kara da cewa, “Mun shiga takarar ne domin mu wakilci Chikun, domin jama’armu su ci moriyar dimokuradiyya kuma a tsakanin ‘yan takara mun yi imanin dan takarar APC zai iya yin hakan.
“Don haka muka ga ya kamata mu mara masa baya domin ya ci zabe. Gwamna Uba Sani ya nuna cewa ya zuwa yanzu ya nuna jajircewarsa mara misaltuwa na bunkasa jihar da kuma tafiyar da kowa da kowa, muna bukatar dan majalisa ya kasance a jam’iyyar siyasa daya da gwamna domin samun saukin ribar dimokuradiyya a mazabarmu.
A wani labarin kuma:Da bamu cire tallafin man fetur ba, da yanzu lalacewar tattalin arzikin Najeriya yafi haka – FG
Gwamnatin tarayya ta ce matsalolin da Najeriya ke fuskanta zai fi ta’azzara idan har da shugaba Bola Tinubu bai cire tallafin man fetur ba.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Malagi, ya ce cire tallafin man fetur ya kasance mafi alheri ga kasar.