Gwamna jihar Ribas, Nyesom Wike ya sanar cewa muddin aka kashe takwaransa na Jihar Binuwe, wato Samuel Ortom, to kuwa alhakin jininsa zai rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya.
A jiya Asabar ne aka kai wa gwamnan Binuwe hari, inda ake yi zargin cewa wasu ’yan bindiga ne suka bude wa ayarin motocinsa wuta a kan titin Makurdi zuwa Gboko da ke Karamar Hukumar Makurdi a jihar.
Sai dai a yayin da yake mayar da martani, Gwamna Wike ya ce idan har aka kashe gwamnan Binuwe, to akwai yiwuwar a sake fafata wani yakin basasa a kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a garin Fatakwal ta jihar Ribas, inda ya ce; idan har kuka kashe Ortom, to ku shirya yi wa Nijeriya jana’iza. “Don muddin wani abu ya sami Gwamna Ortom, alhakinsa zai rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya ne kuma ta tabbata ta zauna cikin shiri don Nijeriya za ta gushe daga kasancewa,” inji shi.
Wike ya kuma yi zargin cewa a lokacin babban zaben kasa na 2019, tsohon Kwamandan rundunar sojin kasa a shiyar Fatakwal, Manjo Janar Jamil Sarham da kuma wasu kusoshin jam’iyyar APC sun kammala shirin kawar da shi daga doron kasa.