Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Larabaya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a gudanar da zabe mai zuwa kamar yadda aka tsara. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar Bishop-Bishop na Najeriya (CBCN) a fadar gwamnati da ke Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za mu ci gaba da daukar kwararan matakai don kare mutanenmu – Abiodun
An dai ci gaba da samun ra’ayoyi mabambanta kan sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi a ranar Litinin da ta gabata cewa zabukan na bana na fuskantar barazanar sokewa ko dage zabe matukar ba a magance matsalar rashin tsaro a sassan kasar nan ba.
Wata majiya a taron ta ce shugaban ya tabbatar wa malaman cewa za a gudanar da zaben kamar yadda INEC ta tsara.
“Shugaban ya ce ranakun da za a gudanar da babban zaben da hukumar zabe ta kayyade abu ne mai kyau kuma ya bukaci kowa ya marawa INEC baya da kuma kokarin ganin an gudanar da zabe cikin lumana, sahihanci da adalci,” inji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina ya fitar, ta ambato shi yana cewa “Boko Haram yaudara ce kuma makarkashiyar ruguza Najeriya ce.”
Ya caccaki akidar kungiyar ta’addanci da ta hana mutane neman ilimi ta yadda hakan ya shafi ci gaban basirar ‘yan kasa.
Shugaba Buhari ya ce za a kara karfafa nasarorin da aka samu a fannin tsaro, kuma za a kara mai da hankali kan tattalin arziki, kafin mika mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Shugaban ya ce an samu ingantuwar harkokin tsaro a tsawon shekaru, musamman a yankin Arewa maso Gabas inda aka mayar da hankali wajen sake gina ababen more rayuwa da kuma mayar da hankali kan ilimi.
A wani labarin kuma, Buhari Ya Taya Shugaban Maajalisar Tattawa Murnar Cika Shekaru 64
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan murnar cika shekaru 64 a duniya. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya ce Lawan na da martabar kasancewarsa daya daga cikin gogaggun ‘yan majalisar Dattijan a kasar nan, inda ya yi shekaru takwas a majalisar wakilai, 1999-2007. , kuma ya kwashe kusan shekaru 12 a Majalisar Dattawa.