Za Mu Tabbatar An Yi Adalci Ga Waɗanda Bam Ya Shafa A Kaduna – Sanatan Kaduna
Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a zauren majalisar, Sunday Marshall Katung, ya ce zai yi aiki tare da sauran ‘yan majalisar tarayya daga jihar domin tabbatar da cewa wadanda harin bam da sojoji suka kai wa a al’ummar Kaduna sun samu adalci.
Rundunar sojin Najeriya a ranar Litinin din da ta gabata ta amince da cewa yayin da dakarunta ke fatattakar ‘yan ta’adda a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Afaka a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, sun yi kuskuren tayar da bama-bamai a wasu mutanen kauyen a wajen wani taron addini.
KARANTA WANNAN LABARIN:Tinubu da Shettima za su kashe N10bn a tafiye-tafiye, yayin tsuntsayen Villa suka samu N201m
A wata sanarwa da ya fitar domin jajantawa al’ummar jihar Kaduna da al’ummar da abin ya shafa, Sanata Katung ya ce za su tabbatar da kula da wadanda suka tsira da rayuwar su.
“Wannan lamarin wani abin takaici ne da kuma koma baya ga sabbin hare-haren da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke kaiwa a yankin, jihar Kaduna da ma kasa baki daya,” in ji shi.
Haka kuma, Sanata Babangida Hussaini (Jigawa North West) ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.
A cikin wasikar ta’aziyya ga Sanata Lawal Adamu Usman (Kaduna ta tsakiya) da al’ummar mazabar sa, Hussaini ya ce ya samu cikin kaduwa, abin takaici da ban takaici na harin bam da aka kai kan mutanen kauyen da ba su ji ba ba su gani ba.
A wani labarin kuma:Dalilin Da Yasa Ta’addanci Ke Ci Gaba Duk Da Kasafin Kudi Masu Yawa – Shugaban Tsaro
Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Janar Christopher Musa ya bayyana dalilan da suka sa har yanzu ba a kawo karshen ta’addanci ba duk da dimbin kason kasafin kudin da sojoji ke samu duk shekara.
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Arise a daren ranar Talata, Musa ya ce sojoji ba su da isassun kayan aikin da za su yaki ‘yan ta’addan, domin duk shekara ba a saki dukkan kudaden da aka ware domin tsaro ba.