“Za mu tabbatar ba a turo mana masu Digirin da ba su cancanta ba” – NYSC
Hukumar da ke kula da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa ba a ba wa daliban da ba su cancanta ba gurbin shiga Hukumar domin yiwa ƙasa hidima.
Darakta Janar na NYSC Birgediya Janar YD Ahmed ne ya bayyana hakan a yau a Abuja yayin taron shekara-shekara na 2023 na ƙungiyoyin kwararru da wasu hukumomin da ke kula da gudanar da shirin.
Shugaban wanda ya yaba da aikace-aikacen kungiyar likitocin hakori ta Najeriya ya kara da cewa shirin ya tsara dabarun da za su rubanya kokarin da suke yi wajen tabbatar da samun takardar shedar sana’o’i daban-daban ga waɗanda suka kammala karatunsu bayan karɓar takardar shedar kammala bautar ƙasar.
Da take magana ta bakin Daraktan ICT Mrs Christy Uba, Daraktar ta bayyana cewa akwai buƙatar masu ruwa da tsaki su ba da goyon baya don tabbatar da burin samar da ci gaba musamman a fannin ilimi da sauran al’umma.
KARANTA NAN:Bayan biyan Miliyan 13, masu garkuwa da mutane sun kuma buƙaci Miliyan 200 kudin fansa
Binciken da aka yi kan ƙoƙarin hukumar cikin shekara biyu na ya nuna cewa an sami babban ci gaba wanda kuma kokarin abin yabawa ne daga dukkan masu ruwa da tsaki da ke tafiyar da hukumar.
Yunkurin da hukumar gudanarwar jami’o’i ta NUC ta yi na ƙoƙarin zaliƙo sunayen Makarantun da ba a amince da su ba abin a yaba ne matuka ganin yadda ‘yan Najeriya ke samun karin bayani kan waɗannan haramtattun makarantu.
Duk da haka wannan bai kawar da ayyukan jami’an da ke kulla alaƙa da wasu jami’o’in ƙasashe maƙwabta masu zaman kan su, tare da baiwa ɗalibai takardar shedar kammala makarantun kasashen waje daga nan Najeriya, irin su jamhuriyar Benin, da Togo, da Cameroun da Nijar da sauransu”, in ji Shugaban.
Darakta Sashen Tantance waɗanda suka kammala Digiri domin shiga shirin bautar ƙasar Hajiya Walida Siddique Isa ta nanata kudurin shirin na tabbatar cewa ƙwararrun masu digiri waɗanda suka cancanta ne kaɗai za su samu damar shiga shirin, domin yin gogayya da takwarorinsu a duk faɗin duniya.
A nasu sakon fatan alheri daban-daban, wakilan hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa JAMB da hukumar kula da Jami’o’i NUC da hukumar Jarabawar NBTE suka yi, sun yaba da tsarin da hukumar NYSC ɗin tayi tare da yin alkawarin ba da goyon baya don ganin an cimma buƙatun da ake buƙata.