Za Mu Yi Aiki Da Tinubu Don Tabbatar Da Zaman Lafiyar Yankin Afirka – Shugabannin APC Mazauna Waje
Kwamitin shugabannin kasashen waje karkashin jagorancin Honorabul Tunde Doherty sun yi alkawarin hada kai da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin yammacin Afirka.
Wata sanarwa a ranar Alhamis mai dauke da sa hannun shugabannin kwamitin da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasashen Gambia, Faransa, Kamaru, Afirka ta Kudu, Switzerland, Dubai, Ireland, Australia da sauran kasashe da dama, ta ce nadin Tinubu a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS zai kara kawo sauye-sauye ga al’amura a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnan APC Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori 11
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan matsayi mai daraja yana nuni ne ga irin gagarumin jagoranci, jajircewarsa, da bayar da gudunmawa mai kima ga hadin kai da ci gaban yankin.
“A matsayinmu na kwamitin shugabannin kasashen waje, mun yi alkawarin bayar da goyon baya da jajircewarmu don yin aiki tare da ECOWAS wajen cimma muradun hadin kan yankin, ci gaban tattalin arziki, da samar da zaman lafiya da wadata a yammacin Afirka.
“ hawansa mukamin shugaban ECOWAS ya nuna wani gagarumin ci gaba a wannan gagarumin aikin nasa, kuma muna da tabbacin zai yi fice a wannan sabon mukamin.
“A karkashin jagorancinsa, muna sa ran cewa ECOWAS za ta sake ganin sabon karfi wajen ciyar da yankin gaba gaba, bunkasa tattalin arziki, da karfafa zaman lafiyar siyasa a tsakanin kasashe mambobin.”
A wani labarin kuma:DSS: Mun gurfanar da Emefiele a Kotu
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ta gurfanar da Godwin Emiefele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a gaban kotu.
Rundunar ‘yan sandan sirrin ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga umurnin wata babbar kotun birnin tarayya Abuja da ta ce a saki Emefiele nan da kwanaki bakwai ko kuma a gurfanar da shi gaban kuliya cikin gaggawa.