Majalisar dattijai ta fara karanta wani kudirin doka da ke ba da shawarar cin tarar N50,000 ga iyayen da suka gaza wajen bai wa ‘ya’yansu makarantun firamare da sakandare.
Red Chamber kamar yada ake kiranta kuma ta ba da shawarar a bada abinci kyauta ga kowane yaro a ƙasar.
Kudirin da Sanata Orji Kalu ya gabatar mai taken, ‘Dokar ilimin bai daya na wajibi na shekarar 2004, sashe na 2’ ya bayyana cewa kowace gwamnati a Najeriya za ta samar da ilimi kyauta, na wajibi da na bai daya ga duk wani yaro da ya kai matakin firamare da karamar sakandare.
Dokar ta ci gaba da cewa duka iyaye su tabbatar da cewa yaransu sun halarci kuma sun kammala karatunsu na firamare da karamar sakandare ta hanyar kokarin tura yaron zuwa makarantun firamare da kananan sakandare.
Karanta nanGwamnan Kano Ya Saka Hannu Akan Karin Kasafin Kudi Na Naira Biliyan 58
Dokar ta ci gaba da cewa masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a karamar hukuma za su tabbatar da cewa duk iyaye ko mutumin da ke da kulawa da yaro ya yi aikin da aka dora masa a karkashin sashe na 2 (2) na wannan dokar.
Dokar ta ci gaba da cewa, iyaye da suka saba wa umarnin da aka ba su zasu fuskanci tarar kudi kokuma dauri a gidan kaso.
Sai dai majalisar dattijai, a gyaran da ta yi, ta gabatar da shawarar tarar Naira 50,000, maimakon N5,000 da aka bayyana a baya a dokar.
Canjin ya ce, “Sashe na (4) (b) na babbar dokar an gyara shi ne ta hanyar cire N2,000 da saka N20,000. Sashi na (4) (c) na babban dokar an gyara shi ne ta hanyar cire N5,000 da saka N50,000.”
Ya kara da cewa, “An gyara sashe na 3 (2) na babbar dokar ta hanyar cire N10,000 da saka N100,000.
A wani labarin kumaRundunar Sojin Nijeriya Ta Bukaci Yan Jarida Su Zama Jakadun Kwarai Ta Hanyar Yada Labaran Gaskiya
Ya ci gaba da cewa mutumin da ya karba ko ya samu wani kudi da ya saba wa tanadin karamin sashe na (1) na wannan sashe ya aikata wani laifi kuma yana da alhakin tarar da ba za ta wuce N10,000 ba ko kuma daurin wata uku a gidan yari ko kuma duka biyu.
Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Kodinetan Shirin Ilimi na Farko a Reform Education, Nigeria, Ayodamola Oluwatoyin, a wata hira da PUNCH ta ranar Asabar, ya lura cewa duk da matakin da ‘yan majalisar suka dauka abin yabawa ne, ya kamata a gudanar da bincike kan harkar karatu a kasar.