Za’a kammala titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano nan da watanni 24 – Umahi
Ministan ayyuka David Umahi, ya ce nan da watanni 24 za a kammala dukkan sassan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Sanata David Umahi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da ya kai ziyarar duba hanyar Abuja zuwa Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamfara: Ba za mu taɓa tattaunawa da ƴan bindiga ba – Gwamna Lawal
Ministan wanda ya samu rakiyar Ministan Kudi da daidaita tattalin arziki Wale Edun ya bayyana cewa gwamnati ta yi sabon wa’adin ne bayan cimma yarjejeniya da dan kwangilar aikin hanyar Julius Berger.
Ku tuna cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da kwangilar ne a shekarar 2018 a kan za’a kammala a cikin watanni 36 amma ta kasa cika alkawari.
Umahi, ya dora alhakin jinkirin da aka samu a kan rashin kudi, yana mai tabbatar da aniyar gwamnati na kawo karshen hanyar a kan lokaci.
Ya ce, “Julius Berger ya amince ya kammala tafiyar kilomita 15 a kullum saboda an amince da sabuwar ranar.
A wani labarin kuma:Gwamna Buni ya amince da biyan Naira miliyan 708 ga ma’aikata 461 da suka yi ritaya
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da kudi N708, 158, 208.77 domin biyan kudaden fansho ga ma’aikata 461 da suka yi ritaya a fadin jihar.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Buni, Mamman Mohammed ya sanyawa hannu ranar Asabar.