Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa (EFCC) ta ce ta kama mutane 12 da ake zargi da sayan kuri’u a zaben ciko da aka kammala ranar Asabar a jihohin Kano da Katsina.
Kwamandan EFCC na shiyyar Kano, Faruk Dogondaji, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, a wata hira da ya yi da manema labarai cewa, an kama wadanda ake zargin da tsabar kudi Naira miliyan 1.5 a jihohin Kano da Katsina.
KARANTA WANNAN LABARIN: Daga Karshe INEC Ta Sanar Da Wanda Ya Lashe Zaben Doguwa/Tudunwada
A cewarsa, an kama mutane 10 ne a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, biyu kuma a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina.
Dogondaji ya ce an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke kokarin jawo masu kada kuri’a da kudade a wasu rumfunan zabe.
Ya ce an kama wadanda ake zargin su 10 ne da Naira miliyan 1,357,500 a karamar hukumar Doguwa, yayin da aka kama mutanen biyu da N242,000 a karamar hukumar Kankia.
“Har ila yau, za mu kasance a jiki a duk cibiyoyin tattara sakamakon don hana canjin sakamako,” in ji shi.
Ya ce kasancewar jami’an a wurin da ake gudanar da zaben zai kara sahihanci ga aikin.
Kwamandan na EFCC ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike. (NAN)
A wani labarin kuma, Ku Bayyana Dan Takararmu A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben da Aka Sake – PDP Ga INEC
Jam’iyyar PDP a jihar Imo ta yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta bayyana dan takararta na majalisar wakilai a mazabar Isu, Modestus Osakwe a matsayin wanda ya lashe zaben da aka sake gudanarwa ba tare da wani bata lokaci ba.
Jam’iyyar PDP ta yi tir da irin tashe-tashen hankula da aka gani a rumfunan zabe hudu da ya kamata a sake gudanar da zabukan a yau.