Akalla kwamishinoni 11 ne suka yi murabus daga mukamansu a majalisar Kwamishinin Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinonin sun hada da na ma’aikatun Fili da gidaje, Aminu Bala Bodinga,; Matasa da Wasanni, Bashir Gorau; Kudi, Abdussamad Dasuki; harkokin tsaro da hukumomin su, Garba Moyi da Kwamishinan Ma’aikatar harkokin addini na jihar ta Sokoto, Abdullahi Maigwandu.
Sauran sun hada da kwamishinonin ayyuka, Salihu Maidaji; Ma’adanai, Abubakar Maikudi; Albarkatun Ruwa, Shu’aibu Gwanda Gobir; Muhalli, Sagir Bafarawa da karamar hukumar, Manir Dan’iya wanda har yanzu mataimakin gwamnan jihar ne da kuma kwamishinan kasuwanci, Bashir Gidado.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ci gaba da cewa Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato Sa’idu Umar Ubandoma da Shugaban Ma’aikatan Gwamnan Jihar Mukhtar Umar Magori su ma sun yi murabus.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa Tambuwal ya amince da murabus din nasu.
A cikin makonni biyun da suka gabata, kusan kwamishinoni 50 ne suka yi murabus a jihohi daban-daban Dake fadin kasar nansaboda zaben shekarar 2023.
Sashe na 84 (12) na dokar zabe ta shekarar 2022 (kamar yadda aka gyara) ya nuna cewa, Babu Wani Dan Takarar da zai tsaya takarar kujerar siyasa ta zabe a zaben shekarar 2023, Kuma Yana rike da mukamin siyasa na nadi.
Bisa jadawalin zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar, jam’iyyun siyasa na da damar gabatar da sunayen Yan takaransu a babban zaben kasarnan zuwa ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2022.
A wani labarin Kuma na daban.
Hamɓararren shugaban NNPP ya janye ƙarar da ya kai Shugaban Jam’iyyar na Yanzu Doguwa
Tsohon shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, da sakatarensa Usman Garko, sun janye ƙarar da su ka kai shugaban jam’iyyar na yanzu, Umar Doguwa.
Wata Babbar Kotun Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Sanusi Ma’aji ta sanya ranar 26 ga Afrilu, 2022, domin sauraren ƙorafin da su ka shigar a kan Shugabannin jam’iyar, ƙarƙashin Umar Doguwa.
Mutanen biyu dai sun shigar da ƙara ne, su na masu neman a dakatar da shugabannin jam’iyyar NNPP, biyo bayan rusa shugabannin jam’iyar da Habib ɗin ya jagoranta.
Habib da Garko sun nemi kotun, gami da dai sauran Ƙorafe-ƙorafe, da ta aiyana zaɓen shugabannin da Doguwa ke jagoranta a matsayin haramtacc, wanda ya saɓawa doka, kuma maras amfani da tasiri kuma ba shi da wani tasiri, inda su ka kuma nemi da kotun ta da ayyana cewa shi ne sahihin shugaban jam’iya.
Sai dai kwatsam, a wani sauyin shawara Habib da Garko sun shigar da wata takarda, mai kwanan wata 26 ga Afrilu, 2022, kan dakatar da ƙarar da su ka shigar a kan NNPP, Doguwa (da sauran mambobin kwamitin zartarwa na jihar Kano) da INEC.
A cikin sanarwar da DAILY NIGERIAN ta samu a yau Laraba, masu shigar da kara sun dogara ne da doka mai lamba 23 na doka ta 1 ta babbar kotun jihar Kano ta shekarar 2014.
Sai dai Habib bai bayyana dalilansa na janye karar ba.
Comments 1