Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Kuma Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, ya bayyana cikakken bayanin ganawar gwamnonin jam’iyyar PDP da Dan Takarar jam’iyar Atiku Abubakar
Tambuwal ya ce Atiku a ranar Laraba ya gana da gwamnoni don tsara dabarun tabbatar da nasarar PDP a zaben 2023 mai zuwa.
Ya shaida wa manema labarai cewa taron ya fi zama na tuntubar juna.
Dan siyasar tare da dan takarar sun zo ne domin gode wa gwamnonin kan rawar da suka taka a wajen taron fidda gwani ni jam’iyar PDP
Tambuwal ya ce, “Mun tattauna ne kan hadin kai da hadin gwiwa wajen ganin an gudanar da yakin neman zabe cikin nasara wanda zai haifar da nasara ga jam’iyyar PDP a zabuka daban-daban daga majalisar dokokin jiha, zaben kasa, gwamna da na shugaban kasa a watan Fabrairun 2023.
“Taron ya yi Mai da hankali wajan tattaunawa kan al’amuran da suka shafi hanyar da za a bi.”
Tambuwal ya kuma bayyana cewa har yanzu Atiku yana tuntubar Wanda zai a’a a matsayin mataimakin shugaban kasa Wanda zasuyi takarar ta dashi.
Tambuwal ya ce “yana daga cikin shawarwarin, ana kuma ci gaba da tuntubar gwamnoni a kan hakan.”
A wajen taron akwai shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sen. Iyorchia Ayu; Gwamna Nyesom Wike na Ribas, Udom Emmanuel na Akwa-Ibom, Samuel Ortom na Benue, Ifeanyi Okowa na Delta, Bala Mohammed na Bauchi da Seyi Makinde na Jihar Oyo.