A kananan hukumomi 12 da aka ayyana ya zuwa yanzu a jihar Legas, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya lashe bakwai yayin da takwaransa, Peter Obi na jam’iyyar Labour ya lashe biyar.
Duk da rasa karamar hukumarsa ta Ikeja da Obi ya yi, har yanzu abubuwa na tafiya yadda ya kamata a jihar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Sakamakon kananan hukumomin da aka sanar sun hada da — Lagos Mainland, Ikorodu, Epe, Ibeju-Lekki, Lagos Island, Badagry, Ikeja, Kosofe, Eti-Osa, Somolu, Amuwo-Odofin da Agege. Akwai kananan hukumomi 20 a jihar.
KARANTA HAKANAN Tinubu Ya Doke Peter Obi A Rumfar Obasanjo
Baya ga Ikeja, inda Mista Obi ya nuna bacin ransa, dan takarar jam’iyyar LP ya kuma yi nasara a kananan hukumomin Kosofe da Somolu, wadanda ake ganin su ne tungar ga APC.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Jarin sunayen kananan hukumomin da aka sanar da sakamakonsu.
Manyan kananan hukumomin Lagos
APC – 20,030
PDP – 3,005
LP – 18,698
NNPP – 257
Adadin kuri’un da suka baci: 43,095
Adadin Kuri’un da aka ki yarda da su: 2,204
Adadin kuri’un da aka kada : 45,299
2. karamar hukumar Epe
APC – 19,867
LP – 3,497
NNPP – 76
PDP – 5221
Adadin kuri’un da suka baci: 29,222
Adadin kuri’un da aka ki amincewa da su: 1,356
Adadin kuri’un da aka kada : 30,578
3. Karamar hukumar Island ta Legas
APC – 27,760
LP – 3,058
NNPP – 79
PDP – 2521
Adadin kuri’un da suka baci – 33,886
Adadin kuri’un da aka ki amincewa da su – 1,052
Adadin kuri’un da aka kada – 34,934
4. Karamar hukumar Ibeju-Lekki
APC – 14,685
LP – 10,410
NNPP – 104
PDP – 2,329
5. Karamar hukumar Ikorodu
APC – 50,353
LP – 28,951
NNPP – 400
PDP – 4,508
6. Karamar hukumar Ikeja
APC – 21,276
LP – 30,004
NNPP – 337
PDP – 2,280
7. Karamar hukumar Badagry
APC – 31,908
LP – 10,956
NNPP – 153
PDP – 6,024
8. Karamar hukumar Agege
APC – 29, 568
LP – 13,270
NNPP – 1,513
PDP – 4,498
9. Karamar hukumar Kosofe
APC – 36, 883
LP – 46,554
NNPP – 903
PDP – 4058
10. Karamar hukumar Eti Osa
APC – 15,317
LP – 42,338
NNPP – 381
PDP – 3,369
11 karamar hukumar Amuwo Odofin
APC – 13318
LP – 55,547
NNPP – 330
PDP – 2383
12 karamar hukumar Somolu
APC- 27,879
Labour Party-28,936
NNNP-476
PDP-3,449.
A Wani Labarin Kuma Saliu Mustapha Na APC Ya Lashe Zaben Sanatan Kwara Ta Tsakiya
Dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC, Mallam Saliu Mustapha, ya lashe zaben Sanatan Kwara ta tsakiya da aka gudanar ranar Asabar.
A ranar Lahadi ne jami’in zabe na INEC, Dokta Nurudeen Bello, ya sanar da sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zaben jihar da ke Omu Aran ranar Lahadi.