Hukumar tsaro ta DSS ta fara gudanar da bincike kan harin da aka kai kan daya daga cikin jami’anta a yayin da ake ta cece-kuce a sake zaben gwamnan jihar Adamawa,Vanguard ta rawaito.
A cikin wani faifan bidiyo da ya bazu, an ga wani jami’in DSS yana hannun wasu ‘yan bangar siyasa a Yola.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Kori Wani Basaraken Gargajiya Daga Mukaminsa
Da yake mayar da martani kan wannan mumunan ci gaban, jami’in hulda da jama’a na hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya,ya ce an fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin amma bai yi karin bayani ba a wata sanarwa daya fitar wanda Vanguard ta samu a ranar Lahadi.
Afunanya ya ce: “An jawo hankalin hukumar tsaron (DSS) kan wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta inda ake zargin wani ma’aikacin hukumar ne a hannun wasu bata-gari na siyasa a jihar Adamawa. Hakan ya biyo bayan ci gaban da aka samu daga karin zaben gwamnan jihar.
“Hukumar na son sanar da jama’a cewa ta fara gudanar da cikakken bincike a kan al’amuran da suka haddasa faruwar lamarin.
“Yayin da ake kira da a kwantar da hankula, rundunar ta kuma bukaci bangarorin da abin ya shafa a jihar Adamawa da su ci gaba da zaman lafiya, su guji tashin hankali,” in ji Kakakin DSS.
A wani labarin kuma, DA DUMI-DUMI: INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kebbi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nasiru Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi.
Jami’in kula tattara sakamakon zabe na jihar Kebbi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.