By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar Ibo don Ci gaban Najeriya ta yi tir da gazawar Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta kasa na rashin bada katin zabe ga wadanda zasu kasance masu kada kuri’a a zaben gwamnan Anambra da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba.
Kungiyar ta nuna damuwa kan rashin sakin katunan zabe na dindindin ga wadanda suka halarci aikin rijistar na baya, ‘yan makwanni kafin zaben, kuma ta bayyana shi a matsayin alama mai hatsari.
Michael Chibuzo, sakataren IPAN na kasa, yace yakamata INEC ta gaggauta rarraba katinan zabe ga masu son yin zabe.
“Ina kira ga dukkan mu damu dage wajen shiga zabe cikin lumana da kowa da kowa tsofaffi, matasa, da mutane na musamman, makomar ta mu ce,” in ji Mista Chibuzo.ya kuma yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri’a don zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba a Anambra da su kasance masu sanya ido don gudanar da ayyukansu na gari ta hanyar yin zabe daidai.
Kazalika IPAN ta shawarci masu zaben Anambra da su tantance ‘yan takarar gwamnan da zasu zaba bisa la’akari da asalinsu, ko na sirri ko na jama’a, don tantance wanda zai iya sarrafa kananan albarkatun jihar.
“Anambra ba za ta iya yin kuskuren wajen jefa kuri’a a cikin wanda ba shi da wata muhimmiyar manufa ga jama’a, wanda kawai ke son a kira shi gwamna amma ba shi da manufa mai ma’ana,” in ji Mista Onuzulike.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa zaben ranar 6 ga watan Nuwamba wata dama ce ta gyara kurakuran da suka faru a baya, yana mai nadama cewa shugabannin Anambra a baya basu mai da hankali kan batutuwan da suka fi muhimmanci ba.