Daga Muhammad Gambo Damaturu.
Gamayyar kungiyoyin matasa da dalibai da masu bukata ta musamman daga mazabar dan majalisar dattawa dake wakiltar Yobe ta gabas sun bukaci Usman Alkali Baba da yafito yatsaya takarar kujerar dan majalisar dattawa a zaben maye gurbin da za’ayi.
Sun bayyana hakanne ta bakin shugabansu Muhammad Baba Isma’il yayin da sukayi gangamin zantawa da yan jaridu a dakin taro na kungiyar yan jaridu dake Damaturu fadar gwamnatin jahar Yobe.
Karanta nanNasarar Sanwo Olu Nasarmu Ce Gaba Daya-Matasan Legas
Muhammad yace duba ga namijin kokari da tsohon sifeton yan sanda na kasa Alkali Usman Baba yayi a lokacin da yake mulki a fannin samar da tsaro sukaga yadace yafito yatsaya takarar kujerar.
Shugaban yakara dacewa zaban senator Ibrahim Gaidam da shugaba Tinubu yayi a matsayin ministan harkokin yan sanda zai baiwa tsohon sifeton damar fitowa yatsaya takara, ya wakilci mazabarsa a majalisar dattawa domin cigaba da aiyukan cigaban al’ummar jihar Yobe.
Saboda haka gamayyar kingiyoyin sun bukaci Alkali Usman Baba da yafito yatsaya takarar idan hukumar zabe tashirya zaben maye gurbin.
A wani labarin kuma
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Akan Maganar Gwamnan Zamfara
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar ikirarin da gwamnatin jahar Zamfara keyi na cewar tana tattaunawa sulhu da yan bindiga a boye a matsayin tsagwaron karya.
Ministan tsaron Najeriya Muhammadu Badaru ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira,inda yace babu wani shiri da gwamnatin tarayya takeyi domin tattaunawa da yan bindigar daji.