Kungiyar Grassroots Movement for Change (GMC) reshen jihar Ekiti, ta gargadi Gwamna Kayode Fayemi kan yin amfani da tsarin gwamnati wajen fifita ‘dan takarar da yake goyon baya.
A ranar Alhamis ne za a gudanar da zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar APC gabanin zaben ranar 18 ga watan Yunin shekarar nan
Sanarwar da GMC ta fitar a ranar Litinin, ta yi nuni da cewa, duk wani yunkuri na kawo cikas ga muradin al’ummar kasar, za a dakile shi.
Sakataren kungiyar, Ademola Ogunrombi, ya ce Fayemi ya samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, don haka bai kamata ya shiga duk wani abu da zai haifar da tashin hankali a jihar ba.
Ya kuma bukaci da a bar mutane su zabi dan takarar da suke so ba tare da fargabar magudi ba.
“Wannan zaben yana neman gabatar da sabon dan takara a karon farko cikin dogon lokaci a tarihin zabenmu.
“Ga wadanda suke neman bautar da mu ta hanyar karbar kudi don jinginar da makomarmu, Ina gargadin cewa Ekiti ba kamar kowace jiha ba ce.” Inji sanarwar
Kungiyar ta bukaci masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye don tabbatar da cewa jihar ba ta shiga cikin rikici ba “saboda son kai na wasu tsiraru”.
Sanarwar ta shawarci kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa a karkashin jagorancin Gwamna Mai Buni da su kasance masu gaskiya da rikon amana a lokacin zaben fidda gwanin.
Tun da farko, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Femi Ojudu, ya shawarci jam’iyyar da ta tabbatar da gudanar da sahihin zabe, domin samar da fitaccen dan takara.
Ojudu ya ce ya yanke shawarar cewa ba zai amince da duk wani mai son tsayawa takara ba saboda yana son ya zama alkali mara son zuciya kuma ya zama wurin hada kai don sasanta sabanin da zai kunno kai bayan zaben fidda gwanin.
A halin da ake ciki kuma, dan majalisar wakilai kuma dan takarar gwamna, Femi Bamisile, ya yi gargadin cewa jam’iyyar APC za ta ruguje idan jam’iyyar ta zabi dan takararta a wajen mazabar Ekiti ta Kudu.
Bamisile ya yaba da amincewa da zaben fidda gwanin Yar tinke, yana mai cewa hakan zai kawar da nauyin kudi a kan ’yan takara da kuma yadda ake yin magudin zabe.
Dan majalisar ya jaddada cewa mutanen Kudu ba za su iya lamuntar “makircin” da ya raba su da ma’auni na siyasa ba tun shekarar 1999.