- Mataimakin sakataren yada labarai na kasa kuma mamba a kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC, Murtala Yakubu Ajaka ya fice daga jam’iyyar.
- Daukar matakin ya biyo bayan hana shi shiga zaben fidda gwani na gwamnan jam’iyyar APC a jihar kogi.
- Rahotanni sun bayyana cewa tsohon dan jam’iyyar APC na shirin share fagen karbar tikitin takarar gwamna na jam’iyyar SDP a zaben gwamnan
Mataimakin sakataren yada labarai na kasa kuma mamba a kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC mai mulki, Murtala Yakubu Ajaka ya yi murabus daga mukaminsa a jam’iyyar.
DAILY POST ta tattaro cewa murabus din Ajaka na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 17 ga watan Mayu 2023 zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa.
KARANTA WANNAN: Yan Majalisar Tarayya 3 da Dubbannin mambobi Sun Fice Daga PDP zuwa APC
Ajaka, a cikin wasikar, ya ce ya kuma aike da wasikar a rubuce ga shugaban jam’iyyar APC na mazabar Ajaka dake a karamar hukumar Igalamela/Odolu ta jihar Kogi.
Wasikar ta ce a wani bangare “Don Allah ka ba ni dama in daukaka irin hazaka ta siyasa wanda mai girma Gwamna, tare da goyon bayan Kwamitin gudanarwa na kasa na yanzu, ya samu nasara da tsayin daka don rubuta fitattun nasarori a zabukan da ya gabata.
“Saboda cike da alfaharin lashe zaben shugaban kasa, na yi imani da cewa jam’iyyar a karkashin ku za ta iya taimaka wa gwamnati mai jiran gado ta inganta tsarin mulki don amfanin ‘yan Najeriya.
“Ni kuma, ta wannan matsakaicin ina fatan in gode wa ‘yan uwana mambobin NWC saboda abokantaka ta musamman yayin da muka yi aiki tare, fatana ne cewa za mu rabu bisa ka’ida, sai dai mu sake haduwa, a kan lokaci.”
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa Ajaka wanda babban dan siyasa ne daga Kogi ta Gabas, an hana shi shiga zaben fidda gwani na gwamnan jam’iyyar All Progressives Congress APC a jihar da aka gudanar a watan jiya.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon dan jam’iyyar APC na shirin share fagen karbar tikitin takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party SDP a zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
A wani labarin kuma, FG Da Likitoci Sun Sanya Hannu Kan Yarjejwniyar Fahimtar Juna, Da Yuwuwar Yanye Yajin Aiki
Akwai yiyuwar likitoci a karkashin kungiyar likitoci masu neman kwarewa a Najeriya NARD su janye yajin aikin da suke yi cikin sa’o’i 48 masu zuwa. Kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Wannan shi ne sakamakon taron sulhu da kungiyar ta yi da gwamnatin tarayya, wanda ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige ya shirya a ranar Juma’a.