Kwamishinan Kananan hukumomi na jihar Murtala Sule Garo yace, zasu cigaba da marawa gwamnan Kano baya a kowane lokaci.
Muratala Garo ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jami’iyyar APC da aka gudanar yau a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnatin jiha.
Garo ya ce a matsayinsa na shugaban kananan hukumomi na jihar Kano zasu cigaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cew ana yin aiki yadda ya kamata a jihar nan.
Ya kuma godewa daukacin ‘ya’yan jam’iyyar bisa yadda suka nuna jajircewa a lokacin da akayi shari’a akan shugabancin jam’iyya a Kano.
Wannan taro na zuwa ne bayan da kotun daukaka Kara, a babban birnin tarayya ta tabbatar da Abdulahi Abbas a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar na jihar Kano.