Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul-Samad Isiyaku Rabiu, ya bayyana cewa kamfanin simintin na BUA ya kammala shirye-shiryen rage farashin simintin da yake yi a fadin kasar nan a wani bangare na tallafawa tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnatin tarayya ta bullo dashi.
Rabiu, wanda ya bayyana haka a ranar Alhamis a wajen babban taron shekara-shekara na Bua Cement karo na 7 da aka gudanar a Abuja, ya ce kamfanin ya kudiri aniyar cimma burinsa ta hanyar inganta yadda ake samar da wadataccen siminti a fadin Najeriya.
KARANTA NANTinubu Ya Nemi Taimakon Majalisar Dinkin Duniya Wajen Yaki Da Ta’addanci A Najeriya
A karshen shekara, muna da niyyar samun karin layukan samar da kayayyaki guda biyu wadanda za su kara karfin samar da a kalla kashi 40 cikin 100 zuwa tan miliyan 70.
Manufar kara karfin samar da kayayyaki ita ce ganin yadda za mu iya rage farashin a bangarenmu don tallafa wa kokarin gwamnatin tarayya akan bunkasa tattalin arziki.
Domin shigo da kayayyaki ba zai zama mafita mafi kyau ba a wajenta dole mu kamfanonin cikin gida mu tallafa mata inji Abdulsamad.
Matsakaicin farashin siminti a Najeriya ya kai N4,500 don haka idan gwamnati ta yi barazanar fara shigo da siminti to za ta kara kashe kudade.
Saboda kudin da ake sayar da su a yanzu ya yi yawa kuma idan ka shigo da shi ta tashar jiragen ruwa dole ne ka biya haraji da sauran abubuwa wanda hakan zai saka siminti ya kara tsada a kasuwannin sayar dashi.
A WANI LABARIN KUMA
Gwamnatin Jahar Gombe Ta Amince Da Karin Albashin Dubu 10 Ga Kowane Ma’aikaci Domin Rage Radadi
Gwamnatin Jahar Gombe A Karkashin Jagorancin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ta amince da karawa kowane ma’aikaci a jahar albashin dubu goma goma tundaga matakin jaha har zuwa karamar hukuma domin tallafawa ma’aikatan wajen rage radadin cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi.