A kokarin da Gwamnan Jihar Kebbi Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu) yake yi na ganin an samar da masu zuba jari a jihar, gwamnan ya kai ziyara wuraren da ake hakar ma’adanai a Warrah da Birnin Yauri a kananan hukumomin Ngaski da Yauri a jihar.
Da yake jawabi a ziyarar dubawa ranar Asabar da ta gabata, Gwamnan ya bayyana cewa, rangadin wani bangare ne na kokarin farfado da ayyukan hakar ma’adanai a yankunan kuma da kara hanyoyin samun kudaden shiga na jihar.
Ya yi nuni da gamsuwa da cewa jihar Kebbi na da hanyoyin samun kudaden shiga da dama baya ga noma, kuma ta kasance daya daga cikin manyan jahohi wajen samar da abinci ga kasa.
Gwamna Idris ya tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta tallafa wa ayyukan hakar ma’adanai ta kowane fanni domin ganin ta tsaya da kafafunta ta kuma ja hankalin masu hakar ma’adinai har ma da masu zuba jari.
KARANTA NANTawagar ECOWAS Ta Gana Da Hambararren Shugaban Kasar Nijar Muhammad Bazoum
Gwamnan ya ce gwamnati mai ci a shirye take ta sake farfado da ayyukan hakar ma’adanai a jihar baki daya domin jawo hankalin masu zuba jari da kuma bunkasa kudaden shiga da jihar ke samu a cikin gida.
Ina so in yi amfani da wannan kafa wajen baiwa matasan da ke gudanar da ayyukan hakar ma’adanai da su kasance masu bin doka da oda da kuma tabbatar da cewa shugabannin al’umma sun gano duk wani sabon da ya shigo yankin domin gujewa duk wani mugun hali.
A yayin da yake zantawa da gwamnan shugaban karamar hukumar Ngaski, Alhaji Abdullahi Buhari Warrah, ya ce an dade ana ayyukan hakar ma’adanai a yankunan, amma ya ce wasu masu hakar ma’adinai sun yi watsi da sana’ar.
Shugaban ya bayyana jin dadinsa yadda sabuwar gwamnati a karkashin Kauran Gwandu ta shirya tsaf domin farfado da harkokin kasuwanci a yankunan.
A WANI LABARIN KUMAMun Shirya Tsaf A Gwabza Damu A Yakin Da Za’ayi Da Kasarmu-Matasan Nijar
Buhari-Warrah ya tabbatar wa Gwamnan cewa majalisar a shirye ta ke ta ba da duk wani goyon bayan da ya dace ga abin da ya bayyana a matsayin gagarumin kokarin da ake.
Wadanda suka halarci taron sun hada da sakataren gwamnatin jiha Alhaji Yakubu Bala Tafida, Hon. Kwamishinan kudi Alhaji Abubakar Chika, kwamishinan ma’adanai da raya ma’adanai Haliru Mohammed Wasagu.