Kungiyar Yan asalin Atyap dake Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jahar Kaduna, sunce zasu yi dukkanin abinda zasu iya domin kare kansu, biyo bayan yawaitar hare-hare da kashe-kashe da Fulani yan ta’adda ke kaiwa.
Idan dai ba’a manta ba, Yan ta’adda sun kai hari a yankin Atyap dake Zangon Kataf, wanda yayi sanadiyyar kashe mutane da lalata gidaje, da wuraren ibada gami da lalata amfanin gona.
Shugaban Kungiyar cigaban yankin Atyap Dr Samuel Achie a jawabin daya fitar, ya koka akan yadda yankin ya zama wurin da Fulani Yan ta’adda ke kai hare-hare, inda ya tabbatar da cewa zasu dauki matakin doka domin kare kansu daga dana sani.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Garkame Wani Jami’in Tsaro Kan Zargin Sace Rodi
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya data kawo masu dauki kafin lokaci ya kure, inda yace da yawa daga cikin mutane, sun rasa gidajen su ba tare da abinci daza su ci ba, biyo bayan yawaitar harin ta’addanci da Fulani Yan ta’adda suke kaiwa.
Achie yace mutanen Atyap masu son zaman Lafiya ne, kuma manoma ne tun asali, amma an raba su da kasar su, inda suke zaune a sansanonin gudun hijira ba tare da tallafin Gwamnati ba, kuma bazasu iya koma wa kauyukan su don cigaba da noma.
Shugaban Kungiyar yace bazasu taba amincewa ba, na yadda cikin kasa da wata daya, sama da mutane 50 sun rasa rayukan su, duk da taron zaman lafiya da Kuma yanayin sha’anin dimokuradiyya a Kasar.
Yace kai harin wanda Fulani yan ta’adda suke yi yana cigaba da gudana, baya ga kashe mutane, sun kuma raunata gidaje da lalata kayayyakin amfanin gona fiye da tunani.