Karamin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Tanko Sununu, ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin tarayya za ta hada Almajirai da yara sama da miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta tare da kafa hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta da nufin a tabbatar sun koyi dabarun da za su dogara da kansu.
Ministan ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar a Sakkwato a wata tattaunawa da Malamai da jami’an gwamnatin Jihar Sakkwato kan kafa Hukumar Almajiri da Yara da ba sa zuwa makaranta.
Ya ce idan gwamnatin tarayya ta kafa hukumar Almajirai da marasa zuwa makaranta ta kasa za a rage yawan Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta da ke yawo a kan titunan birane.
Karanta nanNijeriya Na Gab Da Sayo Jiragen Yaki 6 Daga Turkiyya-Ministan Tsaro
Ina cikin jihar nan ne domin in jawo hankalin Malamai saboda halin da ake ciki na hukumar Almajiri da yaran da ba sa zuwa makaranta da gwamnatin tarayya ta kafa da kuma samun goyon bayanku da hadin kai in ji Ministan.
Muna son dalibanku su samu wasu fasahohin sana’o’i ne kawai bayan kammala karatunsu wanda hakan zai sa su samu abin dogaro da kai da kuma ba su takardar shaida bayan kammala karatunsu.
A cewar Ministan, gwamnatin tarayya za ta fara kaddamar da shirin a Sokoto wanda ya kasance mahaifar fitaccen malamin nan na kawo sauyi Sheikh Usmanu Danfodiyo mai albarka.
Tun da farko a nasa jawabin, sakataren gwamnatin jihar Alhaji Muhammadu Bello Sifawa wanda ya wakilci gwamnan jihar a taron tattaunawa tsakanin Ministan da Malamai da shugabannin makarantu ya ce gwamnatin jihar za ta ba da cikakken goyon baya da hadin kai ga sabuwar hukumar.
Ina da kwarin gwiwa cewa sabuwar hukumar za ta rage rashin aikin yi tare da samar da ayyukan yi a tsakanin daliban da suka kammala karatu tare, Malamai, Almajiri da yaran da ba su zuwa makaranta da za su koyi sana’o’in hannu.
A wani labarin kumaAn Sace Dagaci Da Sauran Mutane A Wani Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Gwamnan jihar Ahmad Aliyu Sokoto ya sanya ilimi a matsayin daya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa.
A nasa jawabin, babban sakataren hukumar Almajiri da yaran da ba su zuwa makaranta Hon Sha’aban Sharada ya ce Najeriya na da yara sama da 500,000 da ba su zuwa makaranta suna yawo a kan tituna.