Shugaba kungiyar kwadago a Najeriya Mr Ajearo yayi barazanar tafiya yajin aikin sai baba ta gani a duk fadin kasar ba tare da baiwa gwamnati sanarwa ba, idan aka sake kara farashin man fetur.
Sai dai fadar shugaban kasa ta mayar da martani cikin gaggawa, ta ce shugaba Bola Tinubu ya damu da matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, kuma yana bakin kokarinsa wajen ganin an daidaita lamarin.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da yan kasuwar mai jiya a Abuja, suka bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kawo karshen tabarbarewar darajar Naira idan aka kwatanta da dala, inda suka ce hakan ya yi tasiri sosai kan farashin man fetur.
Shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, ya yi wannan barazanar ne a lokacin da yake mayar da martani ga shawarar Daraktan kungiyar Kwadago,Emmanuel Igbinosun, na cewa ya kamata ma’aikata su binciko yadda ya kamata ayi kafin fara yajin aikin.
KARANTA NANMajalisar Wakilai Ta Hana Daukar Mutum 300 Aiki Da Hukumar JAMB Ke Shirin Yi
Igbinosun ya ba da shawarar ne a cikin jawabinsa a taron kungiyar kwadagon Afirka da ke gudana a Abuja.
Ajaero ya yi gargadin cewa yan Najeriya sun sha wahala sosai daga manufofin gwamnati kuma ba za su yi na’am da karin farashin man fetur da zai kara ta’azzara lamarin.
Amma ina so ku sani cewa mugayen manufofin tattalin arzikin Najeriya ke cinye albashinmu babu gaira babu dalili.
Idan ka duba waɗannan manufofin da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki da rage darajar kuɗi,sai kafa komai ya lalace.
Idan Naira ta yi daidai da dala a yau, za mu ce ku bar mafi karancin albashi a kan N30,000, zai yi ma’ana. Idan aka duba hauhawan farashin ya koma babu.
Za mu ce ku bar shi a inda yake amma idan farashin ya tashi, idan ma da amincewar Hukumar Kididdiga ta Najeriya, muna da yan Najeriya sama da miliyan 130 wadanda ke fama da talauci. Ina ganin ya kamata ku magance wadannan batutuwa.
Idan muka je a yi ma ma’aikata karin ma’aikata gobe, hauhawar farashin kayayyaki da zai taso zai lalata shi.
Kamar yadda muke a nan a yanzu, suna tunanin kara farashin man fetur kuma ma’aikatar kwadago a wannan lokaci, za su je ma’aikatar shari’a ne kawai domin neman mafita.
A WANI LABARIN KUMAKu Hada Hannu Da Abba Domin Cigaban Jahar Kano-Ganduje Ga Yan Majalisa
Ban so in fadi wasu daga cikin abubuwan da ba za ku ji dadi ba saboda watakila idan sun neme ku ku wakilce su gobe, ba za ku kasance a kusa ba.