Zan ɗora daga inda Badaru ya tsaya – Zababben Gwamnan Jihar Jigawa, Namadi
Zababben gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata nasara ce ga al’ummar jihar.
Namadi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mai taimaka masa kan kafafen yada labarai na musamman da hulda da jama’a ga gwamna Badaru Abubakar Habibu Nuhu Kila wanda kuma aka rabawa DAILY POST ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano Ta Dage Dokar Hana Zirga-zirga Da Ta Sanya
KARANTA WANNAN LABARIN:
Ya ce zaben sa a matsayin gwamnan jihar Jigawa ikon Allah ne.
Ya bayyana godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki da al’ummar jihar da suka ba shi goyon baya da kuma addu’a.
A cewarsa “Ba wai don ina sama da sauran ‘yan takara aka zabe ni ba, sai dai nufin Allah wanda Yake ba da mulki ga wanda yake so.”
Ya yi kira da a yi addu’a daga al’ummar jihar domin ya sauke nauyin da ke kansa.
Namadi ya jaddada kudirin sa na ci gaba da dawainiyar da Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya kafa na tsantseni da shugabanci na gari.
A wani labarin kuma:Zamfara: Lawal na PDP ya doke Matawalle
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara.
Lawal ya samu kuri’u 377,726 inda ya kayar da Bello Matawalle na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, wanda ya samu kuri’u 311,976.