Zanga-zanga ta ɓarke a garin Lafia, bayan sace wasu ɗaliban jami’a
Daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia (FULafia) sun fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da yadda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka ci gaba da yin garkuwa da ‘yan uwansu dalibai.
masu garkuwa da mutane sun kaddamar da hari a wani wurin kwana da ke Gandu, da ke kusa da jami’ar FULAfia, inda suka yi awon gaba da daliban da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:PDP, NNPP da wasu jam’iyyu 5 sun kafa ƙawance
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba.
Majiyoyi sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun kai farmaki gidan da ke wajen harabar, inda suka kama wasu daliban da ba a bayyana adadinsu ba yayin da suka cigaba da harbin iska.
Da suke bayyana bacin ransu da damuwarsu dangane da karuwar rashin tsaro, daliban FULAfia sun fito kan tituna a ranar Alhamis din da ta gabata, suna rike da alluna masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban kamar, ‘Rayuwar Dalibai’, ‘Kukan mutum kukan kowa ne’, da dai sauransu, kuma suna bukatar hakan a gaggauta sakin takwarorinsu da aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba, wadanda a halin yanzu ba a san inda suke ba.
Masu zanga-zangar sun kuma yi kira da a kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi jami’ar, inda suka nuna bacin ransu da yadda ake ci gaba da barazana ga tsaron lafiyarsu.
Sun tabbatar da cewa sun kai makura kuma ba za su iya jurewa matsalolin tsaro da ake fama da su a yankin ba.
Daya daga cikin masu zanga-zangar mai suna Josephine da ta zanta da DAILY POST ta bayyana cewa jami’an gwamnatin jihar sun yi kunnen uwar shegu da halin da suke ciki saboda ba su da alaka da kowa a cikinsu.
“Wannan abu yana kara muni, kullum. Wa ya sani ko za su fara shiga ɗakunan karatu na makaranta don sace dalibai?
“Wanda ake kira Gwamna ya sani amma ya yi shiru bai yi komai ba, domin mu ba ‘ya’yansa ba ne ko kuma danginsa.
“Mun tuna wa Shugaban Jami’ar mu Farfesa Shehu Abdul Rahman, da ya gayyaci Gwamnan makarantar, kuma har yanzu babu abin da ya canza. Muna bukatar dalibanmu da aka sace su dawo da su,” inji ta.
Wani dalibi mai suna Osanga Jacob, ya zargi ‘yan sandan Najeriya da laifin katse musu zanga-zangar lumana.
A wani labarin kuma:Ku gujewa cutar son tara dukiya da yawa – DG ga masu yiwa ƙasa hidima
An shawarci masu yi wa kasa hidima (NYSC) da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu tare da yin hakurin hawa kan matakan samun nasara.
Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Yushau Dogara Ahmed ne ya ba da wannan shawarar a jawabinsa ga masu yi wa kasa hidima na Batch ‘C’ rukuni na biyu na shekarar 2023 a sansanin wayar da kan jama’a na Jihar Nasarawa da ke Magaji Dan Yamusa, Keffi.