Lauyan tsohon firaministan Tunisiya Hamadi Jebali, ya ce alkali ya saki wanda yake karewa, kwanaki hudu bayan da aka tsare shi bisa zargin karkatar da wasu makudan kudade kudade.
Lauyan Mista Jebali ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a makon da ya gabata cewa, an kama wanda yake karewa ne bisa zargin karkatar da wasu kudade.
Rahotonni un nuna cewa, a baya-bayan nan, Jebali ya tafi yajin cin abinci ne domin nuna adawa da tsare shi kuma an kai shi asibiti a ranar Asabar din data gabata.
A lokacin shugabancinsa daga shekara ta 2011 zuwa 2013, Mista Jebali na cikin jam’iyyar Ennahda mai kishin Islama – wadda ita ce, mafi girma a majalisar dokokin kasar har sai da shugaba Kaïs Saïed ya rusa majalisar tare da kwace ikon zartaswa a Tunisia a bara.
A wani labarin kuma na daban.
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa umurnin da ya bayar na yin kira ga mutane da su mallaki makami shi ne su kara kaimi ga kokarin jami’an tsaro a yakin da ake yi da ‘yan tada kayar baya.
Ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin yayin da yake kaddamar da kwamitoci na musamman guda hudu a gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa an kaddamar da kwamitocin ne domin tabbatar da aiwatar da matakan tsaro da ake dauka domin magance matsalar ‘yan fashi da makami a jihar.
Kwamitoci na musamman guda hudu da aka kafa a yau sun hada da Kwamitin tattara bayanan sirri da masu ba da labari na ‘yan fashi, Kwamitin hukunta laifukan da suka shafi ‘yan fashi, Gudanar da Jami’an Kare al’umma da Kwamitin Tsaro na Musamman.
Matawalle ya bayyana cewa, a ‘yan makonnin da suka gabata, Zamfara ta fuskanci hare-haren ‘yan ta’adda a al’ummomi daban-daban, musamman a kananan hukumomin Bukkuyum, Gusau da Gummi na jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da lalubo dabarun murkushe kalubalen tsaro da irin wahalhalun da ‘yan kasar ke fuskanta a hannun ‘yan ta’adda.
Ya yi nuni da cewa gwamnati na sane da kokarin jami’an tsaro wajen magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita, sai dai gwamnan ya bayyana cewa kokarin da sojojin ke yi ya samu cikas saboda rashin kayan yaki na zamani da isassun ma’aikata, don haka ne ya yanke shawarar cewa. jama’a su samo makamai don kare kansu daga ‘yan ta’adda.
Gwamna Matawalle ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samar da motocin Hilux guda 20 da babura 500 ga kwamitoci na musamman domin saukaka musu ayyukansu da zirga-zirga.
Dimokuradiyya ta rawaito Shima da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitocin a yau, shugaban kwamitin na musamman kan yakar ‘yan fashi da makami, Abdullahi Shinkafi ya gargadi masu aikata laifuka da su nisanta kansu daga jihar Zamfara domin lokaci ya yi da za a yi hukunci mai tsauri da duk wanda aka samu da laifi komai girmansa.
Dimokuradiyya ta bada rahoton cewa wannan na zuwa ne kwana biyu da martanin babban hafsan sojojin Kan na Najeriya kan maganar Matawalle na umartar mutanen jihar su mallaki bindiga.
Haka zalika ya baiwa kwamishinan yan sanda umarnin ya bawa mutane lasisin rike bindigar.