Akalla mutane shida, ciki har da matar dan sanda daya aka yi garkuwa da su, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a unguwar Wusasa da ke karamar hukumar Zariya na jihar Kaduna a daren ranar Kirsimeti.
Wata majiya ta shaida wa Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa ‘yan bindigar da suka kai farmakin da misalin karfe 10:30 na dare suna bi gida-gida ba tare da an kalubalence su ba, domin sace mutane.
Majiyar ta ce, matar dan sandan, da ‘ya’yansa mata, da kuma wasu hudu, na daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
Ya ce daga baya jami’an hukumar ‘yan banga na jihar Kaduna (KadVS) sun amsa kiran gaggawa da aka yi musu amma tuni ‘yan bindigar suka tafi tare da wadanda abin ya shafa.
“Yayinda su (KadVS) suka isa suka yi artabu da ‘yan ta’addan a fadan bindiga, sai (’yan bindiga) suka gudu da wadanda abin ya shafa, daga baya aka gane cewa wadanda aka kashen sun fito ne daga gidaje uku daban-daban a unguwar Wusasa,” inji shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya kasa samun amsa kiran waya, ko amsa sakon da wakilin Daily Trust ya aika masa ba.
Idan za’a iya tunawa, ko a ranar 3 ga watan Disamba, shekarar 2021, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu a gundumar Dutsen Abba, da ke karamar hukumar Zariya tare da yin garkuwa da mutane 13, inda suka kashe daya.
Hakazalika, a ranar 14 ga watan Disamba, ‘yan bindiga sun tare hanyar Zaria Kaduna, sun kashe wani dan majalisar dokokin jihar Kaduna tare da yin garkuwa da matafiya da dama.