Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umaru Zulum ya yi wa wani sansanin ‘yan gudun hijira dirar ba-zata inda ya gano daruruwan ‘yan gudun hijira na bogi.
Sanarwar da gwamnatin Borno ta aike wa BBC ta ce daga cikin ‘yan gudun hijira 1,000 da ke cikin kundin jami’an agaji a yankin, 650 daga cikinsu na bogi ne.
Sanarwar ta ce gwamnan ya kai ziyara ne a sansanin kwalejin Mohammed Goni MOGOCOLIS inda ake kula da mutanen karamar hukumar Abadam a arewacin Borno da rikici ya rabasu da gidajensu.Gwamna Zulum ya yi shigar ba-zata ne sansanin ‘yan gudun hijirar da tsakiyar dare tare da rufe sansanin domin tantance yawan ƴan gudun hijirar,” in ji sanarwar.
Sannan ta ce gwamnan ya yi hakan ne domin gano masu karyar cewa ‘yan gudun hijira ne da ke shafe kwanaki a sansanin suna karbar abincin da aka tanadar wa ‘yan gudun hijira, kuma idan dare ya yi su tafi gidajensu.