Gwamnan Jahar Borno Prof Babagana Umara Zulum bayyana haram ta kasuwanci gwan gwan a fadin jahar
Gwamna Babagana Umara Zulum ya sanar da haka ne bayan tantancewar da aka yi na gano wasu tarin karafa da ake kyautata zaton na mallakar gwamnati ne
Gwamna Zulum wanda ke rangadin ayyukan ya ci karo da tarkacen karafa masu yawa, wadanda ake kyautata zaton mallakar hukumomin tarayya ne da kuma gwamnatin jihar Borno
A wata hira da Gwamnan ya yi nuni da cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata an kashe kimanin mutane dubu a jihar sakamakon fasa-kwaurin karafa
KARANTA NANGwamnatin Kogi Tayi Allah-Wadai Da Lalata Ofishin Yakin Neman Zaben SDP
Inda ya kara da cewa mutane na wuce gona da iri a harkar kasuwanci inda ake zargin wasu da sace dukiyar al’umma da suka hada da fitilun titi da tankunan yaki mallakarsu. zuwa kamfanonin sadarwa da sauransu
Gwamnan ya kara da cewa wasu motoci sauke da manyan karafu aka kama kuma ana zargin masu sha’awar sana’ar gwan gwan ne suka mallake su, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta iya bari a ci gaba da ayyukan da ba su dace ba
Daga nan sai ya sanar da haramta ayyukan tsugunar da jama’a a kananan hukumomi ashirin da bakwai da ke fadin jihar
Sannan kuma ta hanyar zartar da dokar da za ta tabbatar da cewa an samu nutsuwa a harkokin kasuwanci da kuma kare rayukan mazauna yankunan
A WANI LABARIN KUMA
Ba Zamu Lamunci Juyin Mulki A Kasashen Afirika Ta Yamma Ba-Shugaban ECOWAS
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya bayyana cewar shugabancinsa na ECOWAS ba zai lamunci juyin mulki a kasashen Afirika ta Yamma ba
Inda yace duk da cewar Dimokuradiyya na da matukar wahalar gudanarwa ya Kamata mutane su yi amanna dashi