Gwamnan jihar Borno Farfesa Zulum ya yi wani likita Bayarabe kyautar mota da kuma kuɗi kusan naira miliyan 14.
Bayanin hakan ya fito ne a sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar inda ta ce gwamna Zulum ya karrama likitan ɗan asalin jihar Ogun ne saboda jajircewarsa duk da rikicin Boko Haram amma bai tsere ba daga aikinsa a babban asibitin Monguno.
Duk da hare-haren Boko Haram amma Dakta Isa Akinbode ya ci gaba da kula da marar lafiya a Monguno a tsawon shekarun da aka shafe cikin rikicin Boko Haram, a cewar sanarwar gwamnatin Borno.
Gwamnatin ta kuma bai wa ‘yarsa a aiki a Jami’ar Maiduguri Gwamnatin ta ce an tattara masa kuɗaɗensa na ladar aikinsa ne inda kuma yanzu za a ci gaba da biyansa duk wata ƙarƙashin wata yarjejeniyar aikin wucin gadi da ya ƙulla da gwamnatin Kashim Shettima.