- Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya kuduri aniyar dasa bishiyu miliyan 10 domin maye gurbin bishiyun da aka yi asararsu sakamakon tashe-tashen hankula
- Gwamnan yace galibin bishiyun da ke kewayen kauyukan jihar an cire su ne saboda dalilai na tsaro
- Amfani da bishiyu wajen sare su don yin makashin abinci ya taimaka wajen samun karancin bishiyu a jihar
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kuduri aniyar dasa bishiyu miliyan 10 domin maye gurbin kashi 80% na bishiyun da aka yi asararsu sakamakon tashe-tashen hankula a jihar, Tribune Online ta rawaito.
Da yake magana a ranar Litinin a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Borno da ke Maiduguri a yayin kaddamar da gangamin yakin neman zabe na shekarar 2023, inda ake sa ran za a dasa bishiyu miliyan 1.2 a fadin jihar, Zulum ya bayyana cewa, gangamin na da nufin dakile kwararowar hamada da sauran matsalolin muhalli a yankunan jihar.
KARANTA WANNAN: Tawagar FG ta Ziyarci Iyalan Marigayi Pa Akinkunmi Wanda Ya Zana Tutar Najeriya
Ya yi nuni da cewa, galibin bishiyun da ke kewayen kauyukan jihar an cire su ne saboda dalilai na tsaro, wasu kuma an sare su ne saboda itace.
A cewar Zulum, gangamin dashen bishiyun na bana a jihar Borno yana da taken “Bishiyoyi don sake tsugunar da jama’a” wanda ya yi daidai da babban taken Majalisar Dinkin Duniya: “Let’s Green Our City”.
Yayin da yake bayar da shawarar yin amfani da tukunyar gas da murhu mai inganci sabanin yadda ake yawan amfani da itacen wuta daga sare bishiyu, Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin dasa bishiyu miliyan 10 nan da shekara ta 2024.
“Idan ba a kula da saran bishiyu ba, wata rana za mu iya gano cewa duk jihar Borno hamada ce. Dukkanmu muna sane da cewa mun yi asarar fiye da kashi 80% na bishiyu a jihar sakamakon tashe tashen hankula.
“Duk bishiyar da ke kewayen kauyukanmu an sare su ne saboda dalilai na tsaro, wasu kuma an sare su ne saboda itace”.
“Batun sauyin yanayi da kwararowar hamada ya kasance babban abin damuwa ga daukacin al’ummar jihohin Arewa, yana mai cewa akwai bukatar a kamo matsalar sauyin yanayi a jiharmu ta hanyar dasa bishiyu”
“A cikin bishiyoyi miliyan 10, kowacce daga cikin kananan hukumomi 27 za ta yi noman bishiyu 200,000 domin samar da bishiyu miliyan 5.4, yayin da gwamnatin jihar za ta yi noman bishiyoyi kusan miliyan 5”.
Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Muhalli ta Jihar da ta yi watsi da kamfen din dashen bishiyu na gargajiya ta hanyar kirkiro wani tsari mai inganci.
Ya kuma bukaci ma’aikatar da ta fito da kalandar aiki wanda ya kamata a bi shi sosai.
Zulum ya bukace su da su tabbatar da cewa ma’aikatar da kananan hukumomi 27 sun yi noman shukar bishiyu tun da wuri domin a fara dashen bishiyu a farkon shekarar 2024.
A wani labarin kuma, Zimbabwe: Bayan Adawa da Zaben Mnangagwa, An Rantsar da Shi A Matsayin Shugaban Kasa
An rantsar da shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a wani sabon wa’adinsa na biyu
Hakan na zuwa ne bayan da masu sa ido na kasa da kasa suka yi zargin cewa zaben kasar bai cika ka’idoji ba
Shugaban mai shekaru 80 a duniya ya ce zai tabbatar da kiyaye kundin tsarin mulkin kasar da kuma bin doka da oda a sabon wa’adinsa
An gudanar da bikin rantsar da shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a wa’adinsa na biyu a ranar Litinin, duk da bayanan da masu sa ido na kasa da kasa suka yi na cewa zaben kasar na watan Agusta bai dace ba.
Mnangagwa ya ce Zimbabwe ta nuna “dimokuradiyya tare da balaga” a yayin bikin a filin wasa na kasa a Harare babban birnin kasar.