Jami’an hukumar Zabe Mai zaman kanta ta kasa Basu Sami damar isowa da wuri ba, yayin da Ake kokarin fara kada kuri’a a zaben Gundumomi na babban Birnin Tarayya Abuja, kamar yadda wakilin Jaridar Punch ya ruwaito lokacin da ya Isa wasu rufunanZabe.
Musali a runfunan Zabe Mai lamba PU157, PU 158, PU 156 da kuma PU 021 dake Gundumar Abuja Municipal, jami’an sun iso ne da musalin karfe 9 da Mintina 23 na safe.
Yayin da aka fara tantancewa dakuma kada kuri’a da misalin karfe 10:45.
Kazalika a rufan zaben Alayeta dake Makarantar Furamarin Chika , jami’an hukumar Zaben wato INEC sun iso ne da musalin karfe 10 na safe.
A runfunan Zabe Masu Lamba 11 da kuma 12 dake Karu Babu ko Jami’i daya daya Isa wurin da misalin karfe 8:30 na safe, yayin da kuma hukumar tace za’a fara kada kuri’a ne da misalin karfe 8 na safe.
Yayin da kuma tuni aka toshe hanyar zuwa babban filin sauka da tashin jiragen Sama na Kasa, bayan da hukumomin Babban Birnin Tarayya Suka bayyana dokar takaita zirga-zirgan kamar yadda Kwamishinan Abuja Babaji Sunday ya bayyana.
Agefe guda Kwamishinan ya ce an Sanya dokar ne sakamakon wasu bayanai dake nuna cewa, matagari na Shirin hargitsa zaben
Akalla Yan Takara 478 ne suke fafatawa a zaben da suka fito daga jam’iyun siyasa 14, a zaben Gundumomi 6 dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
Comments 1