Jam’iyyar PDP a ranar Talata ta bayyana alhininta da damuwarta bisa rasuwar jagora a bangaren watsa labarai, jagoran kasa, kuma dan kasuwa, sannan tsohon ministan ruwa, Malam Isa Funtua.
Sakataren watsa labaran jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce jam’iyyarsu na mika sakon ta’aziyya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa wannan rasuwar, wanda suka bayyana shi a matsayin wani makusancin shugaban kasar.
Ologbondiyan ya ce za a ci gaba da tuna Funtua a matsayin mutumin da ya taka rawa daban-daban wajen ci gaban kasarnan. PDP ta ce gudummawar da ya bayar abin a yaba ne, musamman yadda yake jigo a ‘International Press Institute (IPI)’ da kuma kungiyar mawallafan jaridu na Nijeriya NPAN.
A karshe PDP sun mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalan Mallam Isa Funtua da kuma jagororin kafafen watsa labarai da gwamnatin jihar Katsina.