Phrank Shaibu, mai taimaka wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce kalaman Festus Keyamo a kan shugabansa da cewa alamu ne na rashin amfani da ilimi yadda ya kamata.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa, a kwanakin baya Keyamo ya ce Atiku dan takara ne mara tabbas, don kuwa a baya yayi an gani ba tare da yabawa ba, yana mai cewa har Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, yana gaban Atiku ta fuskar cancanta.
Sai dai da yake mayar da martani a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Shaibu ya ce kalaman bai kamata ace sun fito daga bakin wani ministan tarayyar Najeriya ba.
Da Alama Yarjejeniyar Nukiliyar Iran na Dab da Tabbata Idan …
Ya ce, “Kun san alamar jahilci ne a lokacin da wani minista a Tarayyar Najeriya ke magana da irin wannan yare, Eh yaya za ka tashi ka ce iyaye su roki ASUU su janye yajin aikin.
Ya manta cewa tsarin ilimi yana cikin mummunan yanayi, Makarantunmu da jami’o’inmu ba su da kuɗi kuma ba su da kuɗin inganta su.
“Da farko idan kun san matsayin mataimakin shugaban kasa, kar ku manta cewa Atiku Abubakar ba mataimakin shugaban kasa ne kawai ba.