An kama wani matashi dumu-dumu yana ƙoƙarin sace janareton wata kotu a jihar Ogun.
Matashi mai suna Folorunsho Olaniyan, mai shekara 28 a duniya, an kama shi hannu dumu-dumu ne yayin da yske shirin yin awon gaba da janareton kotun Ado-Odo, cikin ƙaramar hukumar Ota a jihar Ogun.
KU KARANTA KUMA: Wani magidanci ya kai kan sa barzahu bayan sun samu saɓani da matar sa
Jaridar The Punch ta rahoto cewa rajistaran kotun, Kareem Tolulope, shine ya cafke Olaniyan wanda ɗan asalin Ota ne.
Wata majiya ta bayyana cewa wanda ake zargin a ranar Talata, 24 ga watan Janairu, ya shiga ɗakin da ake ajiye janareton bayan ya kwance makullin ƙofar.
Majiyar tace wanda ake zargin yayi amfani da hutun da gwamnatin jihar ta bayar domin karɓar katin zaɓe, wajen aikata laifin sa.
Wata ma’aikaciyar ƙaramar hukumar, Mercy Ajewole, ta tabbatar da cafke wanda ake zargin.
Ta bayyana cewa Olaniyan ya amsa cewa ya shiga sakatariyar ne ta hanyar haura katangar ginin, inda ta ƙara da cewa tuni aka miƙa shi a hannun ƴan sanda.
“Abubuwan da aka samu a hannun sa sune sukundireba guda biyu da jaka.” A cewar ta.
Ba a samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi, har zuwa lokacin kammala haɗa wanna rahoton.
Dalilin Da Ya Sanya Gwamnonin APC Suka Ƙi Goyon Bayan Osinbajo -Naja’atu Muhammad
Tsohuwar mamba a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Hajiya Naja’atu Mohammed, ta bayyana dalilin da ya sanya gwamnonin APC suka ƙi marawa mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, baya.
Hajiya Naja’atu ta bayyana cewa gwamnonin sun ƙi marawa Osinbajo baya saboda ya ƙi ya cika musu aljihun su da kuɗi. Rahoton jaridar Legit.ng ya tabbatar.
Farfesa Yemi Osinbajo, ya sha kaye a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, a hannun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.