Ƙasar India ta yi nasarar tura wani ƙumbo izuwa duniyar wata inda kuma tuni ya yi nasarar sauƙa lami lafiya ba tare da wata tangarɗa ba.
Wannan nasara ta ƙasar Indiyar ta sa ta zama ƙasa ta hudu a duniya da ta yi nasarar tura ƙumbon kuma ya sauƙa lafiya.
KARANTAWANNANLABARIN: Za Muyi Amfani Da Fasahohin Zamani Wajen Yaki Da Miyagun Laifuka A Najeriya-Hukumar Yan Sanda
A lokacin da yake shirin sauka kumbon mai suna Chandrayan 3 ya sassauta saurinsa har sai da ya kai ga bai fi saura mita ɗari ɗaya tsakaninsa da doron watan ba sannan ya sauka cikin nasara.
Wannan aiki dukkaninsa ne an yi shi ne ta hanyar sarrafa kumbon daga nesa.
Indiya ta samu nasarar yin hakan ne yan kwanaki bayan da Rasha ta yi yunkurin yin hakan amma kuma haƙarta ta gaza cimma ruwa.
Sai dai duk da wannan rashin nasara ta Rasha, hakan bai hana shugaban ƙasarya Vladnir Putin taya Indiyar wannan gagarumar nasara da ta samu ba.
“Wannan gagarumar nasara ce, na tayaku murna matuƙa, gaskiya abin abun burgewa ne matuƙa, mun kuma ji daɗi sosai”
Firaiministan Indiya Narendra Modi ya ce gagarumin aikin ƙasar ya bayar da fifiko ga amfani da fasahar ɗan’adam don haka nasarar ta ƴan ƙasar ne da ƙasar baki ɗaya.
A yanzu haka dai kumbon na shirin tura wata na’ura da za ta lalubo inda ake da ƙanƙara abin da zai ba shi damar kafa mazauni na dindindin bisa doron wata.