Ƴan bindiga sun Hallaka Ɗan Sanda a Delta, sun tsere da bindigu
Akwai zaman ɗar-ɗar a yankin Uti na Effurun a Ƙaramar Hukumar Uvwie ta Jahar Delta a ranar Lahadi, a yayinda ƴan bindiga suka harbe wani Ɗan Sanda da aka ɗauko shi a Babur, tare da guduwa da bindigun shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Harin Cocin Ondo: Najeriya Ba Zata Mika Wuya Ga Miyagun Ba——- Shugaban Kasa Buhari
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sun raunata matuƙin Mashin ɗin a lamarin daya faru da misalin ƙarfe 11 na safe.
Jaridar The PUNCH ta gano cewa Ɗan Sandan yana ɗauke da bindigu guda biyu, ɗaya bindigar ta wani abokin sa ne da baya wajen aikin sa, a yayinda ɗaya tashi ce.
An kuma gano cewa matafiya kan hanya sun gudun ceton rai, a yayinda suka shaida harba bindigar.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar DSP Bright Edafe ba’a same shi ba, domin jin ta bakin sa ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Comments 1