Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi, ya yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa masu ibada a cocin St Francis Catholic da ke titin Owa-luwa a masarautar Owo, na jihar Ondo.
A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanya wa hannu, shugaban ya ce, “Koma yaya, kasar nan ba za ta taba mika wuya ga miyagu ba, kuma duhu ba zai taba cin nasara ba. Najeriya za ta yi nasara a karshe.”
Sanarwar mai taken ‘Shugaba Buhari ya jajanta wa wadanda suka mutu, ya kuma jajantawa gwamnatin jihar Ondo da jama’a.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun harbe sama da mutane 25 da suka hada da yara kanana, inda suka bude wuta a yayin da ake gudanar da ibada Lahadi a Cocin na mako-mako.
Da yake mayar da martani game da lamarin, shugaban ya bayyana cewa ƴan ta’addane ne kawai za su iya aiwatar da wannan mugun aiki; suna tabbatar da cewa baƙin ciki na har abada h na jiransu a nan duniya, da kuma a ƙarshe a lahira
Buhari, wanda ya jajanta wa wadanda suka mutu, ya jajantawa iyalansu, cocin Katolika, da gwamnatin jihar Ondo, inda ya bukaci hukumomin da su gaggauta daukar matakai, tare da kawo dauki ga wadanda suka jikkata.
Comments 1