Ƴan bindiga sun kashe mai Karɓar Haraji, da wasu mutum 3 a Benue
Ƴan bindiga a ranar Laraba da yamma sun kashe wani mai karɓar Haraji da wasu mutum 3 a Ƙauyen Kundi dake Mazaɓar Mbacher na Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala ta Jahar Benue.
Mazauna ƙauyen sun yi zargin cewa, mambobin sun kasance ƴan dabar, Ƙasurgurmin Ɗan ta’addan da aka kashe Terwase Akwaza da akafi sani da Gana, wanda aka kashe a ranar Asabar a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jirgin Qatar Airways Zai fara Jigila daga Jihar Kano
Al’ummar sun yi imanin cewa sabon kisan ya kasance ɗaukar fansa akan kisan da Sojoji suka yi, ƴan kwanaki da suka gabata.
Amma Sojoji da farko sun shaidawa Manema Labaru cewa an kashe mutane uku ƴan bindiga a ranar Alhamis da Juma’a a lokacin da Rundunar Soji ta Operation Whirl Stroke tayi bata kashi dasu.
Kwamandan Dakarun Sojin Manjo-Janar Kevin Aligbe yace an gudanar da samamen a yankin bawai don abinda ƴan bindiga suke yi, yana mai cewa tuni ake ragargazar su a yankin, yana mai shan alwashin gano su.
A lokacin da aka tuntuɓe shi akan Lamarin, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Benue SP Catherine Anene bai maido da kira ba, ko saƙon da aka tura mashi a lokacin haɗa wannan rahoton.