Wasu ƴan daba a kan babur din Adaidaita Sahu da ake kyautata zaton masu ƙwacen waya ne sun tare ma’aikaciyar kamfanin jaridar Daily Trust a Kano, Zainab Yusuf, tare da raunata ta bayan sun kwace mata jaka.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, lamarin ya faru da Zainab, wacce ke aiki da sashen gudanarwa na kamfanin ne da safiyar Juma’a lokacin da take hanyar zuwa wajen aiki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta bada Umarnin tsare Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Rivers ga Ƴan Sanda
A cewar jaridar, ƴan dabar su uku sun cimma Zainab ne a babur din a daidai katangar rukunin kantinan Ado Bayero Mall da aka fi sani da Shoprite, lokacin da take kokarin karawasa ofis bayan sauka daga Adaidaita Sahu.
Jaridar ta jiyo ta bakin Zainab na cewa, “Suna zuwa waje na sai mutum biyu suka sauka. Daya ya fara jan jakar dake hannu na nima ina ja yayin da shi kuma dayan yake ta kokarin sai ya caka min wuka.
“Da farko fuska ta ya dinga hari ina kaucewa, sai ya fara kokarin soka min a gefen cikina yayin da na fadi kasa wanwar duk da haka ban saki jakar ba ina ta gocewa.
“Yayin da naga ya fara harin wuyana ne na saka hannu na. Hakan ta sa ya yanke min dan yatsa ya kuma yanke ni a hannu da kafa suka tafi da jakar,” inji ta.
Sai dai ta ce ƴan sa’o’i bayan faruwar lamarin, an tsinci jakar tata a gefen titi a unguwar Sharada.
Wadanda suka tsinci jakar sunyi amfani da shaidar wurin aikin ta domin tuntuba da mayar mata da kayan ta.
Sai dai ta ce barayin sun yi awon gaba da wayar ta kirar iPhone da kudi kimanin Naira 20,000.